'Yan majalisa sun sake bijire wa Trump
February 12, 2019Talla
Gabanin cikar wa'adin iya sake fuskantar tarnaki a harkokin gwamnatin Amirka, Sanatocin jam'iyyun Republican da kuma na Democrats, sun cimma yarjejeniya kan bai wa gwammatin Shugaba Donald damar amfani da wasu kudade wajen gudanar da aikace-aikace.
Sai dai bayanai sun ce 'yan majalisar sun yi fatali da bukatar shugaban kasar na dala biliyan 5 da miliyan 700 da sunan gina ganuwa tsakanin Amirkar da kasar Mexico.
Babu dai tabbacin ko shugaban na Amirka Donald Trump zai amince ya sanya wa yarjejeniyar 'yan majalisar da suka cimma a daren da ya gabata, hannu.
Wannan batun ne ma ya janyo dakatar da ayyukan gwamnati a Amirkar na tsawon kwanaki 35 a makonnin baya, tsayuwar da ba a taba ganin irinta ba a tarihin kasar.