SiyasaJamus
'Yan jarida sun lashe kyautar Nobel ta bana
October 8, 2021Talla
An bayyana wata 'yar jaridar kasar Philippines, Maria Ressa da kuma Dmitry Muratov dan kasar Rasha, a matsayin wadanda suka lashe kyautar Nobel a bana.
An karrama 'yan jaridar biyu ne saboda kwazonsu wajen kare 'yancin aikin jarida da ma na fadin albarkacin baki.
Maria Ressa dai na aiki ne a matsayin shugabar wata jaridar Intanet da ke binciken kwa-kwaf da ake kira Rappler, yayin da shi kuwa Dmitry Muratov ke matsayin babban editan jaridar Independent a Rasha.
Kwamitin bayar da lambar yabon ta Nobel a kasar Norway, ya ce mutanen biyu hazikai ne da suka cancanci karramawa a wannan zamani da aikin jarida da tsarin dimukuradiyya ke fama da matsaloli.
Akalla dai 'yan jaridar za su samu kudaden da za su kai euro dubu 985.