1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar rasa 'yancin zama dan kasa a Indiya

Mohammad Nasiru Awal AS
July 30, 2018

Matakin janye 'yancin zama dan kasa da Indiya ta dauka ya shafi Musulmi tsiraru da ke zaune a jihar Assam mai makwabtaka da Bangladesh wadda aka kafa a shekarar 1971.

https://p.dw.com/p/32LfC
Indien Assam Registrierung  National Register of Citizens
Hoto: Reuters

Kasar Indiya ta yi amfani da wani kundin rajista na wucin gadi da ake takaddama kai, inda a fakaice ta janye 'yancin zama dan kasa na mutum miliyan hudu masu asali da kasar Bangladesh da ke zaune a jihar Assam.

A sabuwar rajistar ta 'yan kasa a jihar da ke arewa maso gabashin Indiya, an sanya sunayen mutum kusan miliyan 29 maimakon miliyan 33. Yanzu ya zama dole wadanda sunayensu ba su bayyana a rajistar ba, su da cikakkiyar shedar cewa iyalinsu na zaune a Indiya gabannin kafa kasar Bangladesh da ke makwabtaka da jihar ta Assam, a shekarar 1971.

Idan ba su yi haka ba suna fuskantar barazanar kora daga Indiya zuwa Bangaladesh. Matakin ya fi shafar Musulmi tsiraru masu magana da harshen Bengali. Sai dai 'yan Hindu masu matsanancin ra'ayin kishin kasa na ganin matakin a matsayin abin da ya dace a gaggauta daukarsa.