'Yan gudun hijirar na komawa ga matsugunansu
January 23, 2016Talla
A cewar daya daga cikin hukumomin birnin na Gamboru Ngala da bai so a bayyana sunansa ba, 'yan watanni uku na baya-bayan nan dai an samu akalla 'yan gudun hijira dubu 15 da suka ketara wannan gada da ta raba garin Gamboru Ngala da Fatokol na kasar Kamarun, inda ya ce a halin yanzu suna da yawan 'yan gudun hijirar da ke ci gaba da dawowa matsugunansu.
'Yan kunguiyar Boko Haram dai sun hallaka mutane fiye da dubu 17 a yankin arewacin Najeriya yayin da wasu fiye da miliyan biyu da rabi suka guje wa matsugunansu tun daga shekara ta 2009.