1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

'Yan gudun hijira sama da 100 sun halaka

Gazali Abdou Tasawa
September 11, 2018

'Yan gudun hijira sama da 100 daga kasashen Afirka sun halaka bayan da jiragen ruwan da ke dauke da su suka nutse a gabar ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/34eUK
Libyen Tote Flüchtlinge an der Küste nahe Zawiya
Hoto: picture alliance/AP Photo/IFRC/M. Karima

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta Medecin Sans Frontiere wacce ta sanar da wannan labari a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Litinin, ta ce lamarin ya wakana a safiyar daya ga wannan wata na Satumba. 

Kungiyar ta ce daga cikin 'yan gudun hijirar da hadarin ya rutsa da su a akwai 'yan asalin kasashen Sudan da Mali da Najeriya da Kamaru da Ghana da Libiya da Aljeriya da kuma Masar. 

Kungiyar ta Medecin Sans Frontiere ta ce jirgin da ya yi hadarin na dauke da fasinjoji 165, kuma 55 daga cikinsu suka kubuta da suka hada da mata masu juna biyu da kananan yara har ma da jarirrai. Sai dai daga cikinsu kimanin 20 sun ji rauni.