1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Indiya: 'Yan majalisa biyu daga gidan kaso

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 5, 2024

Wani dan siyasa daga bangaren 'yan tawayen Sikh da kuma wani daga yankin Kashmir na Indiya, sun bar gidajen kasonsu na dan lokaci karkashin takaitaccen beli domin rantsuwar kama aiki a matsayin 'yan majalisar dokoki.

https://p.dw.com/p/4hvxJ
Indiya l Zabe | Sikh | Amritpal Singh | Gidan Kaso | Sheikh Abdul Rashid | Kashmir
Guda daga cikin 'yan majalisun da suka lashe zabe a gidan kaso a Indiya Amritpal SinghHoto: Narinder Nanu/AFP via Getty Images

Wannan na zuwa ne bayan da mutanen biyu suka samu nasara a zaben da ya gudana cikin watan Yunin da ya gabata, duk da cewa suna tsare a gidan kaso. An dai cafke dan siyasa Amritpal Singh mai shekaru 31 a duniya  a bara, bayan jami'an 'yan sanda sun kwashe tsawon wata guda suna farautar sa. Sai dai duk da haka ya samu nasara a zaben, inda ya maka 'yan takara 26 da kasa tare da lashe kujerar majalisa a jihar Punjab. A nasa bangaren Sheikh Abdul "Engineer" Rashid da ya kasance tsohon dan majalisa a yankin Kashmir da ke karkashin Indiya, an cafke shi ne sakamakon zargin da ake masa da daukar nauyin 'yan ta'adda. Sai dai duk da yana tsare, ya lashe zabe a matsabarsa ta Himalaya mai cike da rikici da kuri'u sama da dubu 200. Baki dayan mutanen biyu dai ba a yanke musu hukunci kan laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba, wanda hakan ya ba su damar tsayawa takara a zaben da suka samu nasarar lashewa.