'Yan fafutuka sun karbi lambar Nobel
December 10, 2018Likitan nan dan kasar Kwango da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya wato Nobel Peace Prize a Turance saboda yadda ya taka muhimmiyar rawa a kokari na ganin an kawo karshen aikata fyade da sauran nau'ika na aikata lalata a fagen yaki, a wannan rana ta Litinin bayan karbar lambar girmamawar ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su tashi tsaye wajen kawo karshen cin zarafi da lalata da ma tallafa wa wadanda aka ci zarafinsu.
Dakta Denis Mukwege, da ya kafa asibiti a gabashin Kwango ya taimaka wa dubban mata da suka fuskanci tozartawa a tashin hankali da kasarsa ta fiskanta a tsawon sama da shekaru 20. Mukwege, tare da Nadia Murad 'yar fafutuka daga kasar Iraki sun karbi kyautar ta Nobel a birnin Oslo na kasar Norway, kyautar da aka kiyasta ta da Dalar Amirka miliyan guda wacce za su raba su biyu.
Dakta Mukwege, ya kalubalanci al'ummomin kasa da kasa saboda kin yin abin da ya dace a tsawon sama da shekaru 20 da kasar ta Kwango ta dauka tana fama da tashe-tashen hankula nan da can, mata na ganin nau'ika iri-iri na cin zarafi.