1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun sake garkuwa da matasa

January 3, 2015

Ta'adin Boko Haram na kara ta'azzara a cikin yankin arewa maso gabashin Najeriya inda suke ci gaba da sace mutane da kisan Kai.

https://p.dw.com/p/1EEXd
Hoto: picture alliance/AP Photo

Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan bindiga da suka kutsa wani kauye na yankin Jihar Borno sun yi awon gaba da matasa maza kimanin 40, abin da jami'an tsaro suka danganta da kungiyar Boko Haram mai dauke da makamai, wadda ta yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.

Mazauna garin Malari da suka tsere zuwa Maiduguri bayan faruwar lamarin, sun ce lamarin ya faru a daren shiga sabuwar shekara, kuma yaran da aka yi awon gaba da su sun hada da 'yan shekaru 10 da haihuwa, inda ake kyautata zaton tsagerun sun kai su dajin Sambisa. Garin na Malari yana da nisan kilomita 20 daga dajin na Sambisa kuma yana kusa da garin Gwoza wanda tsagerun na Boko Haram suka mayar karkashin ikonsu. Yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya yana ci gaba da fuskantar hare-hare daga 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal