1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar

March 10, 2019

Ma'aikatar tsaro a Jamhuriyar Nijar, ta sanar da rasa sojojin kasar akalla bakwai tare da garkuwa da daya, a wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai yankin Diffa da ke a kudu maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/3EjhG
Nigeria Soldaten
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Mayakan na tarzoma sun kai harin ne wani wajen da ake kira Gueskerou da ke cikin yankin na Diffa, inda sojojin a nasu bangaren suka yi nasarar kashe 'yan bindigar 38.

Yankin na makwabtaka da cibiyar Boko Haram da ke a arewa maso gabashin Najeriya. An kuma yi nasarar kwace motoci biyar daga maharan da kuma makamai a cewar ma'aikatar ta tsaro.

A farkon watan Janairun bana, sojojin kasar ta Nijar suka kashe sama da 'yan kungiyar ta Boko Haram 280 a wasu hare-hare da suka kai masu ta sama da kuma kasa. Sabon harin dai shi ne na biyu cikin kasa da wata guda da aka gani a yankin na Diffa.