Yan bindiga sun yi garkuwa da faransawa ukku a Niger Delta
September 22, 2010'Yan fashin jiragen ruwa a Niger Delta sun yi awon gaba da ma'akaitan wani kamfanin da ke kula da harkokin jiragen ruwa na Faransa guda ukku a wani jirgin ruwa. Hari na biyu ke nan da ke faruwa a mako guda a yankin Afirka ta yamma, bayan da aka cafke wasu ma'aikatan Faransar biyar na kamfanin AREVA mallakar Faransa da ke Arlit a arewacin Niger.
'Yan fashin sun kama ma'aikatan ne bayan da suka kai hari wa jirgin Faransar a ƙananan jirage da makamai. Mai magana da yawun rundunar tsaron ko ta kwana, ya ce kawo yanzu mutun huɗu ne aka kama.
A yanzu haka dai, Kamfanin kula da harkokin jiragen ruwan mai suna Bourbon da hukumar harkokin wajen Faransa sun yi magana da iyalen waɗanda aka cafke kuma suna aiki da hukumomi a ƙasar Najeriya domin sako ma'aikatan.
Mawallafi: Pinaɗo Abdu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi