'Yan bindiga sun yi awon gaba da Dr Shettima Ali Monguno
May 3, 2013Yau da rana ne wasu 'yan bindigan da ba'a san ko su wanene ba suka yi awon gaba da tsohon ministan man fetur na Najeriya a Jamhoriya ta farko, Dr Shettima Ali Monguno a unguwar Mafoni bayan ya fito sallar juma'a.
Dr Ali Monguno mai shekaru 92 na haihuwa ya yi suna saboda rawar da ya taka a fannonin illimi da siyasa, kuma yana kan gaba wajen fafutukar samar da zaman lafiya a jihar Borno da kewaye da ma ƙasa baki ɗaya.
Kawo yanzu dai ba'a riga an gano dalilin yin awon gaba da tsohon ministan ba, sai dai rundunar haɗin gwuiwar tsaro ta JTF daga farkon wannan makon ta yi gargaɗin cewa mai yiwuwa ƙungiyar Boko Haram ta yi kame dan samun kuɗin fansa.
Husseini Monguno wani mai sharhi kan tsaro da al'amuran yau da kullun daga jihar Bornon ya tabbatar da afkuwan lamarin, ya ce kawo yanzu babu masaniyar inda ya ke sai dai har yanzu suna jira su ji ko waɗanda suka ɗauke shi za su yi waya tunda yana ɗauke da wayar hannunsa a cikin aljihu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar