1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun halaka masu aikin riga-kafin Polio

Ramatu Garba Baba
April 27, 2019

Pakistan ta bayar da umarnin dakatar da riga-kafi na allurar cutar Polio na gama gari da aka kaddamar bayan wasu hare-hare da suka janyo kisan wani ma'aikacin jinya da wasu jami'an 'yan sanda da ke tsaronsu.

https://p.dw.com/p/3HYrq
Pakistan Polio Impfung
Hoto: Getty Images/AFP/A. Ali

Masu da'awar jihadi a yankin na zargin cewa allurar Polio,  shiri ne na hana 'ya'yansu haihuwa. Kasashen Pakistan da Afghanistan da kuma Najeriya na daga cikin kasashen duniya da suka rage da cutar ta Polio ta zama annoba.