'Yan bindiga sun halaka limami a Batsari
July 30, 2020'Wasu ‘yan bindiga sun halaka malamin addinin Musulunci da wani farar hula daya a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina a yankin Arewa maso yammacin Najeriya. Wannan harin da ya salwantar da ran limamin Jumma'a Malam Tukur ya faru ne cikin daren Laraba zuwa wannan Alhamis inda maharan suka bude wa limanan wuta bayan da suka afka masa, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba
Hare-hare da sace-sacen mutane don neman kudin fansa na neman zama ruwa dare a yankin na Batsari da kewaye tun bayan tabarbarewar harkar tsaro a Zamfara da katsina. Sai da a lokacin da DW ta tintibi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina SP Isa Gambo don jin matakin da aka dauka, ya ce shi ma zai tuntubi baturen 'yan sandan yankin dan jin abun da ya faru kafin yayi Karin haske.