An kai hare-haren kan masallatai a Najeriya
December 4, 2022An kai harin ne a garin Ughelli da ke jihar Delta a Kudancin Najeriya, wasu 'yan bindiga ne suka bude wuta kan masallatai bayan da masallatan suka yi yunkurin hana tafiya da limamin masallacin, kafin daga bisani su yi garkuwa da mutum uku, a yayin da suka raunata akalla mutum goma sha daya da ke kwance a asibiti a cikin mawuyacin hali a yanzu. Alhaji Badamasi Saleh, shi ne shugaban 'yan arewa mazauna jihar Edo da ke makwabtaka da jihar ta Delta ya tabbatar wa wakilinmu na Naija Delta Mohammed Bello yadda lamarin na ranar Asabar ya auku.
Hakazalika a Najeriya, a ranar Asabar da ta gabata, wasu 'yan bindiga sun bude wuta a wani masallaci, a daidai lokacin da jama'a ke Sallar Isha'i a yankin Funtuwa da ke jihar Katsina, inda suka kashe limamin masallacin tare da yin garkuwa da masallata akalla goma sha takwas.