1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan awaren Mali sun kashe gomman sojoji

October 1, 2023

Kungiyoyin 'yan awaren Abzinawa a Mali sun yi ikrarin yin mummunar barna kan sojojin kasar, a wani hari da suka kai a tsakiyar kasar da ke yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4X0xk
'Yan tawayen Abzinawa na kungiyar CMA
'Yan tawayen Abzinawa na kungiyar CMAHoto: SOULEYMANE AG ANARA/AFP/Getty Images

Tun da farko, Abzinawan sun ce sun kashe dakarun sojin kasar kimanin 100. Ikrarin hakan na zuwa ne a cikin sanarwar da kungiyar CMA ta fitar.

Sai dai kawo yanzu ba a tabbatar da ikararin 'yan awaren ba sakamokon matsaloli da suka haifar da rashin isa wurin. Rundunar sojin Mali dai ta sanar da cewa an kai wa sansanin sojinta da ke yankin Mopti hari a ranar Alhamis din da ta gabata, ba tare da wani karin bayani ba. 

Karin bayani: Tsageru suna kara kaimi a Mali

Idan aka tabbatar da ikrarin kungiyar ta CMA, zai kasance hari na baya-bayan nan da Abzinawan suka kai tun bayan dawo da zafafa kai hare-hare kan dakarun Mali da ke arewacin kasar a watan Agusta.

Karin bayani: 'Yan tawaye sun kashe sojojin Mali 

Ana dai ganin hakan ba ya rasa nasaba da janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA daga kasar tun bayan da sojoji suka karbe ikon kasar.