'Yan Aljeriya ba sa so Bouteflika ya zarce
March 1, 2019'Yan sandan kasar Aljeriya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa 'yan kasar da suka mamaye kofar ofoshin Firaminista don nuna adawa da neman wa'adi na biyar na mulki da shugaban Abdelaziz Bouteflika ya yi. Ba a dai bayyana ko wadanda ke neman tserewa sun ji rauni ko sun yi asarar rayuka ba. Sai dai Kamfanin dillanacin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa dubban 'yan Aljeriya sun fantsama kan titunan Algiers da wasu garuruwan kasar don nuna adawa da manufofin gwamnatin da ke ci a yanzu.
Tun a ranar 10 ga watan Fabirairu ne Bouteflika ya bayyana aniyar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasar da zai gudana a ranar 19 ga watan Afirilu, duk da shanyenwar barin jiki da yake fama da shi. Ranar Lahadi ce ranar karshe da doka ta amince ta ajiye takardun takara a gaban kotun tsarin mulki.