Gabon: 'Yan adawa na ikirarin lashe zabe
September 1, 2023Jam'iyyun adawan na Gabon sun yi tsokaci a karon farko tun bayan juyin mulki kasar, inda suka yaba da matakin da sojojin suka dauka domin kare dimukuradiyya. Sai daga bisani sun kuma bukaci sojojin da su tabbatar da nasarar da dan takararsu Albert Ondo Ossa ya samu a zaben kasar da aka gudanar a rnanar Asabar (26.08.23) wanda ya bar baya da kura.
Karin bayani: Sojoji sun yi juyin mulki a Gabon
Wannan furici na jam'iyyun adawan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon jagoran sojojin ya fara girka sabbin hukumomin mulkin rikon kwarya tare da daukar sabbin kudurori, ciki har da canja ranar bikin samun 'yancin kan kasar daga 17 ga watan Ogusta inda mayar da shi izuwa ranar 30 ga watan Agusta, wacce ta zo daidai da ranar da aka hambarar da shugaba Ali Bongo.