1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita wa'adin zabe a Zambiya

Yusuf BalaJanuary 21, 2015

'Yan sanda a Zambiya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa 'yan adawar kasar da ke zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/1EOZ0
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/J. Schoonees/Gcis

'Yan jam'iyyar adawar ta UPND dai na yin wannan zanga-zanga ne bisa abun da suka kira shirya yin magudi a zaben shugaban kasar biyo bayan sakamakon zabuka na farko da aka fara fitarwa wanda ke nuni da cewa jam'iyya mai mulki ta PF ce ke kan gaba a zaben. Dubun-dubatar masu kada kuri'a ne suka yi sammakon zuwa rumfunan zaben kasar domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da zai maye gurbin marigayi Micheal Sata da ya rigamu gidan gaskiya a watan Oktoban bara.

Sambia Wahlen Unruhen 2006
Hoto: AP

Neman canji daga masu kada kuri'a

Da dama daga cikin masu kada kuri'unsu da aka tatauna da su sun bayyana cewa sun doko sammako ne domin su yi wannan zabe cike da fatan samun canji daga halin da kasar ta samu kant a ciki na tsahon shekaru ukun da suka gabata. Yanayi dai ya kawo nakasu ga mafiya yawan masu kada kuri'a sakamakon ruwan sama mai karfin gaske, wanda ya tilasta tsawaita wa'adin kammala kada kuri'un da a fafatawar da ake yi tsakanin Patriotic Front mai mulki da Edgar Lungu mai shekaru 58 ke wa jagoranci da Hakainde Hichilema na jam'iyyar UPND mai adawa da tsahon yini guda.

'Yancin zabe ga ko wanne dan kasa

A cewar Emma Mwanza da ke fafutukar kare demokradiya a kasar ta Zambiya satar kuri'u ba zai hanasu zabar wanda suka yi niyya ba.

Präsidentschaftswahl in Sambia Michael Sata Wahlsieger
Hoto: dapd

Ta ce: "Akwai alamu na yin wani dabarun satar kuri'a wannan abu ne da ba za a lamunta ba dole mu zabi wanda mu ke so, wannan abu ne da ba za amu amince da shi ba."

An dai tanadi kananan jiragen ruwa da amalaken shanu dan samu akai ga hanyoyi da wuraren da ruwa ya hana motocin ma'aikatan zabe kai kaya zuwa runfunan zabe.