1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zabe cikin halin rashin tabbas a Kamaru

Abdul-raheem Hassan MA
September 21, 2018

A hukumance a ranar Asabar ne ake fara yakin neman zaben shugaban kasa a Kamaru. Sai dai akwai rashin tabbacin tsaro a yankunan da ke amfani da Turanci Ingilishi zai janyo wa zaben nakasu.

https://p.dw.com/p/35JOn
Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Masu zanga-zanga a yankin da ke amfani da Ingilishi a KamaruHoto: Getty Images/AFP

Daruruwan mutane a yankin kudu maso yammacin garin Buea, na tserewa sakamakon fargabar tashe-tashen hankula gabannin zabukan kasar. Gwamnan yankin Bernard Okalia Bilai, wanda ya tabbatar da tsayuwar gwamnati wajen samar da tsaro, na neman hanyoyin da za a bi don kwantar wa masu niyan hijira hankali don komawa gidajensu.

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Sai dai John Nlom, da ke dab da tsallakawa tare da iyalansa, ya ce bai yadda da tabbacin samar da tsaro daga gwamnatin ba. Sama da makonni  uku kenan gwamnatin ta ce dubban mutane suna na hijira. Jama'a ba su damu da zancen kuri'a ba, inda suke zargin rashin adalci a zaben.

 

Shugaban jam'iyyar USDP Prince Ekosso ya shaida wa tashar DW cewa:

"Ba zai yiwu a samu sahihin zabe yankunan Arewa maso yamma da Kudu maso yammacin Kamaru ba, maganar gaskiya, garuruwan da ke wadannan yankunan sun tarwatse. Maganar samun ingantaccen zabe a yankunan ba mai yiwuwa bane. An makara wajen yin abin da ya kamata ya tabbatar da samun zabe na gaskiya."

'Yan takara da dama ne dai ke ziyartar yankunan da ake samun tashin tashina a Kamarun, da zimmar ba su kwarin gwiwar kada kuri'unsu a ranar zaben, yankunan kuma da ake gani da wuya Shugaba Paul Biya ya kai ziyarar yakin neman zabe a cikinsu. 'Yan takara Takwas ne dai ke neman takarar da Shugaba Paul Biya wanda ya shafe shekaru 36 a kan mulki.