Yakin neman zabe a kasar Gabon
November 24, 2005Talla
Ranar lahadi ce mai zuwa idan Allah ya kai mu, a ke shirya zaben shugaban kasa a Gabon.
A halin da ake ciki jam´iyu daban daban na ci kin yakin neman zabe, saidai masu kulla da a al`ammuran siyasar a kasar sun tabbatar da cewa, babu shaka Shugaba Omar Bango za shi tazarce a wannan mukami.
Omar Bango na da shekaru 28 daidai bisa karagar mulkin kasar Gabon, idan a ka zabe sa ranar 27 ga watan nobemba, zai kara wasu shekaru 7.
Jam´iyun adawa sun zargi shugaban kasar, da anfani da dukiyar jama´a, a cikin yakin neman zabe.
Kamar yadda dokoki su ka tanada a Gabon, zagaye daya kawai a keyi a zaben shugaban kasa, matakin da ke kara tabatar da shugaba mai ci yanzu za shi tazarce.