1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cutar amosanin jini ta yi kamari a Yuganda

October 1, 2019

Gwamnatin Yuganda ta karfafa matakan gwajin cutar amosanin jini a kasar, bayan da wani bincike ya gano cewa duk shekara ana haifar jarirai kusan dubu 20 dauke da wannan cuta ta Sikila a kasar.

https://p.dw.com/p/3QYmx
Elfenbeinküste Krankenhaus
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Wani bincike da aka gudanar a kasar Yuganda ya nunar da cewa duk shekara ana haifar jarirai kusan dubu 20 dauke da cutar amosanin jini (sikila). Kuma abin da ya fi daga hankalia cikin matsalar shi ne yadda kaso 80 daga cikin 100 na wadannan jarirai ke mutuwa kafin jarirran su shekara biyar a duniya. A kan haka ne gwamnatin kasar ta dauki matakin karfafa yin gwajin cutar musamman a kan sabbin haihuwa.

Cutar amosanin jini ciwo ne da matsaloli cikin jini ke haifarwa wanda ke hana kwayoyin hallittar jikin dan Adam samun wadatacciyar iskar Oxygen da jiki ke bukata.Galibin  masu wannan larurar, na fama da yawaitar kamuwa da kwayoyin cuta na Bacteria da na Malaria, radadin jiki da na kasusuwa da sauran cututtuka masu barazana ga rayuwa. Kananan yara na yawan koke-koke saboda radadin ciwo da suke fama da shi. A sashen kula da masu cutar amosanin jini na asibitin Mulago da ke Kampala, babban birnin kasar Yuganda kusan kullum ana samun marasa lafiya sama da 100 da ke jiran ganin likita. Mwanaid Zainab, daya daga cikin masu jiran, na da yaro dan shekara biyu da ke fama da cutar, ta kuma bayyana nadamarta ta rashin yin gwajin cutar, wanda da ta yi shi, da yaronta ba zai fuskanci wanann wahala ba:

Mosambik Kinderklinik
Hoto: picture-alliance/dpa

"Haka kwatsam kawai yake kama kuka a kullum, ba irin kukan da aka saba ji ba kuwa, kukan na ciwo ne, a wurinmu ni da mijina ba mu san batun gwajin jini na kwayoyin halitta kafin aure ba. Sai dai yanzu kawai babu abin da ya wuce yin abin da ya dace wajen kulawa da dan namu."

Kwamishinan ma’aikatar lafiya, Dr Patrick Tusiime, ya bayyana cewar ma'aurata da dama na shiga wannan matsalar ce saboda rashin sanin cutar, wanda hakan ya haifar da yawaitar masu larurar amosanin jinin. Ya ce a saboda haka ne gwamnati ta kara karfi a tarukan wayar da kan al'umma game da cutar kafin aure:

"Da zarar mutum ya san yana dauke da kwayoyin cutar, sai ya kiyaye wajen zabar mata ko mijin aure, saboda idan mutum ya zabi mai dauke da kwayoyin cutar, yiwuwar haifar 'yaya masu dauke da amosanin jinin na da yawa. 

Blut - Transfusionsmedizin
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Hoppe

Trevor Waiswa, wani dan shekaru 17 da ke kwance a asibitin na Mulago sakamakon cutar amosanin jini, ya bayyana yadda yake shan wahala wajen yin abubuwan yau da kullum na rayuwa. Ya ce ba ya iya daukar abu komin rashin nauyinsa saboda yadda yake jin rashin kwarin jiki, ko tafiya ba ya iyawa, ga yawaitar jin sanyi da yake. Hakan ya sa duk sati sai ya karbi magunguna.Amma a bangaren wani mai dauke da cutar, Felix Luswata, ya bayyana cewar don nisanta kansa da yin rashin lafiya ko da yaushe, ya lakanci bin dokar likita da cin abinci mai kyau wanda ya ce ita ce mafita da ke taimakonsa yake samun damar yin sabgoginsa na rayuwa:

"Ina shan maganina kullum na Folic acid, sannan ina shan kunnun gero wanda yana dauke ne da sinadarin Iron, hakan kuma na taimakona, sannan ina shan ruwa sosai, ina kuma kiyayar abubuwan sha na gwangwani saboda suna da illa ga lafiyarmu."

Dr Patrick Tusiime ya ce har yanzu dai ba su fitar da rai ba na raguwar wanann cuta saboda gwamnatin kasar ta fitar da wani sabon magani mai suna hydroxyurea, maganin da ke jirkita cutar, wanda nan ba da dadewa ba zai isa zuwa ga cibiyoyin ba da magani.