Yajin aiki ya kassara hada-hada a filayen jirgin saman Jamus
April 27, 2016An soke tashin daruruwan jiragen sama a fadin kasar Jamus bayan da ma'aikatan gwamnati suka fara wani gajeren yajin aiki a wannan Laraba. Yajin aikin da ya zo gabanin fara sabon zayagen tattaunawa kan karin albashin ma'aikata, ya shafi manyan filayen jiragen saman kasar a birane guda takwas ya kuma kassara harkokin sufurin motocin safa da jiragen karkashin kasa a wasu garuruwa. Kusan jiragen sama 400 ne aka soke tashinsu a filin jirgin saman birnin Fankfurt kawai, bayan da ma'aikatan kwana-kwana a filin jirgin saman suka ajiye aikinsu. Dubun dubatan fasinjoji dai sun shiga halin kakani-kayi, kamar yadda wannan fasinjan ya nunar.
"Ba na tausaya wa masu yajin aikin. Ko da suna son karin albashi ai babu dalilin saka dubban fasinjoji cikin kunci. Ba na jin wannan matakin ya dace."
Yajin aikin ya kuma shafi zirga-zirgar jiragen sama a biranen Munich da Kwalan da Düsseldorf da Hannover da Bremen da Berlin da kuma Hamburg.