1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki ya janyo cikas a filin Jirgin saman Frankfurt

February 28, 2012

Yajin aiki a filin jirgin saman Frankfurt na Jamus na janyo asarar kuɗi Euro miiyan ɗaya a kowace rana

https://p.dw.com/p/14B7G
Hessen/ Eine Flugzeug der Fluggesellschaft Lufthansa landet am Freitag (17.02.12) auf dem von der Fraport AG betriebenen Flughafen in Frankfurt am Main waehrend eines Streiks der Vorfeldbeschaeftigten. Die Beschaeftigten auf dem Vorfeld des Frankfurter Flughafens haben seit Donnerstag (16.02.12) nach einem Aufruf der Gewerkschaft der Flugsicherung (GdF) die Arbeit niedergelegt. (zu dapd-Text) Foto: Mario Vedder/dapd
Filin jirgin saman FrankfurtHoto: dapd

Ma'aikata a babban filin jirgin saman birnin Frankfurt dake nan Jamus, waɗanda ke ci gaba da gudanar yajin aiki sun janyo - ala tilas- aka soke jigilar ɗaruruwan jirage a wannan Litinin, wanda kuma zai yaɗu ya zuwa Talatar nan musamman ga jiragen da za su yi jigilar cikin gida a Jamus da kuma a tsakanin ƙasashen tarayyar Turai. Ƙungiyar ma'aikata ta GdF tana shirya jerin yaje-yajen aikin ne bisa irin kuɗaɗen albashin da ake baiwa ma'aikata a filin jirgin, waɗanda ba na cikin jirgi ba, da kuma akan yawan sa'oin aikin su.

A baya bayannan ne kuma ƙungiyar ma'aikatan ta ce akwai muhimmancin gaske jami'an dake kula da sauka da tashin jiragen saman su bi sahun yajin aiki na tsawon sa'oi shidda a safiyar wannan Larabar domin nuna goyon baya ga 'yan uwansu. Matakin dai ka iya janyo mummunar matsala fiye da wadda ake fama da ita a yanzu. Kamfanin Fraport dake da alhakin tafiyar da harkokin filin jirgin saman na birnin Frankfurt ya ce salon yajin aikin na yanzu yana janyowa kamfanin asarar kuɗi kimanin Euro miliyan ɗaya a kowace rana.

A yanzun nan da ake batu dai hukumomin filin jirgin na yin amfani da ma'aikatan da ba su da wakilci a cikin ƙungiyoyin ƙwadago domin maye gurbin masu yajin aikin da nufin gudanar da jigilar kashi 80 cikin 100 na adadin jiragen saman da za su tashi, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙaucewa cuskoson matafiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu