1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki na ci gaba da kamari a Lufthansa

Abdul-raheem Hassan
November 28, 2016

Kamfanin Lufthansa zai ci gaba da dakatar da zirga-zirgan jiragen sama da 1,700 da ke shirin tashi a ranakun Talata da Laraba sakamakon yajin aikin ma'aikatansa.

https://p.dw.com/p/2TOra
Deutschland Flughafen Frankfurt
Hoto: picture alliance/dpa/B. Roessler

Wannan yunkurin na zuwa ne bayan da kamfanin Lufthansa ya gaza gabatar da kwararan hujjoji a gaban kotun da'ar ma'aikata da ke Frankfurt na bukatar takawa yajin aikin birki. Direbobin jiragen sun shiga yajin aikin ne tun ranar Laraba da ta gabata bisa rashin cimma matsaya a kan biyan wasu kudade da suke bukata daga kamfanin.

Ana ganin ci gaba da wannan yajin aikin zai shafi akalla fasinjoji 180,000 wanda hakan ke zama babbar nakasu ga kamfanin. Wannan shi ne karo na hudu da matuka jiragen ke shiga yajin aiki tun bayan da suka gabatar da bukatunsu na karin kaso 3.66 cikin dari na albashi a duk shekara wanda ya kai su fara juya wa kamfanin baya a watan Afirilun shekara ta 2014.