'Ya kamata a binciki Isra'ila kan zargin kisan kare dangi'
November 17, 2024Fafaroma Francis ya nuna goyon baya ga bukatar kaddamar da bicike kan zargin da ake yi wa Isra'ila na kisan kare dangi a zirin Gaza a cikin wani littafinsa da ya ke sa ran wallafawa kamar yadda jaridar Italiya ta La stampa ta ruwaito.
A cewar wasu daga cikin kalmomin da littafin ya kunsa abinda ke faruwa a Gaza ya na da alamun kisan kare dangi, dan haka akwai bukatar duba shi da tsanaki domin ganin ko ya yi dai-dai da abinda alkalan wasu kotunan duniya suka fada.
Paparoma ya nemi afuwar yaran da aka ci zarafinsu a coci
Isra'ila na sha suka a duniya saboda yawan fararen hula da yakin da take yi a Gaza ya shafa da kuma karancin kayan agaji.
Kasar Afirka ta Kudu ce ta gurfanar da Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague bisa zargin kisan kare dangi.
Fafaroma ya yi tir da kisan faren hula a Gabashin Kwango
Babban mai shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya nemi a kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Gallant da kuma shugabannin Hamas.