1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yarejejeniyar kasuwanci ta duniya

Abdul-raheem Hassan
June 17, 2022

Kungiyar cinikayya ta duniya, ta amince da wani shiri wanda ba a taba ganin irinsa ba na yarjejeniyoyin cinikayya da suka shafi kiwon lafiya da wasu gyare gyare da kuma samar da abinci.

https://p.dw.com/p/4CpxO
Schweiz | WTO Konferenz in Genf | Ngozi Okonjo-Iweala
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

An dai cimma yarejjeniyar ce bayan rashin jituwa tsakanin kasashe 164 kan muhimman batutuwa da suka tilastawa kungiyar tsawaita tattaunawar zuwa kwanaki biyu.

Yarjejeniyar ta zo ne bayan da Shugabar kungiyar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala ta bukaci kasashen da su sasanta, bayan da aka kasa cimma matsaya kan kawo karshen tallafin kamun kifi da ke illata muhalli da kuma watsi da cikakken ikon mallakar magungunan COVID-19.

Tattaunawar da ta kunshi ministocin cinikayya fiye da 100 ana kallonta a matsayin muhimmiyar dama da kungiyar cinikayyar ta iya kulla yarjejeniyoyin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban.