1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta fitar da rahoto kan cutar Ebola

December 27, 2014

Hukumar ta lafiya ta ce mutanen da suka rasu sakamakon cutar a Afirka sun kai akalla 7.693 daga cikin adadin mutane 19.695 da suka kamu da cutar a duniya.

https://p.dw.com/p/1EAYB
Hoto: Reuters/Denis Balibouse

A rahoton da ta fitar a ranar Jumma'a, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce kasar Saliyo da ta fi kowace kasa tabuwa da wannan cuta, ta sanar a ranar 24 ga watan Disamba cewa ga baki daya mutane 9.203 ne suka kamu da cutar, daga cikinsu 2.655 suka rasu. Yayin da kasar Laberiya da aka fi samun mace-mace, ke da adadin mutane akalla 7.708 da suka kamu da cutar daga cikinsu mutum 3.384 suka rasu. Sai kuma kasar Gini da ke da adadin mutane 2.630 da suka kamu da cutar, inda daga cikinsu 1.654 suka rasu.

Bayan wadannan kasashe dai, an samu akalla mutane shidda a kasar Mali, daya a Amirka sannan takwas a Najeriya da suka rasu sakamakon cutar ta Ebola. A wani kiyasi da aka bayar a ranar 21 ga watan Disamba, akalla jami'an kiwon lafiya 666 ne suka kamu da cutar ta Ebola daga cikinsu 366 suka rasu. Ga ga baki daya dai mutane 7.708 ne suka rasu a fadin duniya sakamakon kamuwa da cutar ta Ebola.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal