WHO ta fara amfani da maganin gwajin Ebola
January 8, 2015Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa a kokarin da masana harkar hada magunguna suka kammala, a yau Alhamis cikin wannan wata za a fara aiki da allurar gwajin. Idan har aka ga nasarar maganin gwajin maganin zai wadata watanni kadan baya.
Kimanin kwararru 90 ne daga kamfanonin hada magunguna da cibiyoyin lafiya da ma'aikatun lafiya suka hadu a hedikwatar Hukumar ta Lafiya ta Duniya WHO don yin nazari kan maganin gwajin kafin a fara amfani da shi a kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea. Tuni dai wannan cuta ta Ebola ta hallaka sama da mutane dubu takwas a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.