1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Bukatar kawar da maganin jabu

January 24, 2023

Gurbatattun maganin tari na da alaka da mace-macen yara a nahiryar Afirka da Asiya kamar yadda binciken hukumar lafiya da duniya WHO ya nunar

https://p.dw.com/p/4MdMz
Symbolfoto I Hustensaft
Hoto: Markus Mainka/Zoonar/picture alliance

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta bukaci daukar matakan gaggawa domin kawar da gurbatattun magungunan da aka danganta da mace-macen daruruwan yara a Afirka da nahiyar Asiya.

Yara fiye da 300 ne suka rasu sakamakon gurbataccen maganin tari a kasashen Gambiya da Uzbekistan da Indonesia a shekarar 2022.

Da dama daga cikin yaran basu wuce shekaru biyar da haihuwa ba.

Ana kyautata zaton lamarin yana da  dangantaka da gurbataccen maganin tari da aka yi a Indiya da Indonesiya da wasu sinadarai masu matukar hadari.