1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An bai wa Hukumar Abinci ta Duniya kyautar Nobel

Ramatu Garba Baba
October 9, 2020

Kwamitin Kyautar Nobel ya bayar da kyautar zaman lafiya a bana ga Hukumar Abinci ta Duniya da ke kai dauki ga wadanda ke da tsananin bukatar taimako na abinci a kasashen da ake fama da rikici ko matsalar yunwa.

https://p.dw.com/p/3jgRn
Afghanistan UN-Welternährungsprogramms (WFP) in Kabul
Hoto: picture-alliance/dpa/AFP/Nemenov

Hukumar Abinci ta Duniya wato WFP ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel da aka sanar a wannan Juma'a a birnin Oslo na kasar Norway. An bai wa hukumar kyautar bisa kokarinta ne na wadata jama'a da kayayyakin agaji tare da rage matsalar yunwa a yankunan duniya da ake fama da matsaloli na rikicin yaki ko karancin abinci.

A bara kadai, mutum akalla miliyan dari da ke a kasashe kimanin tamanin da takwas a sassan duniya hukumar ta wadata da abinci da wasu kayayyaki na agaji don rage raddadin kuncin da suka samu kai.

Kwamitin mai bayar da kyautar ta Nobel ya ce hukumar ta cancanci kyautar, ya kuma ja hankulan duniya kan miliyoyin da har yanzu ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen da rikici ya daidaita. Kwamitin ya ce Hukumar Abinci ta Duniya ta yi amfani da ayyukanta a wani kokari na samar da zaman lafiya ta kulawa da wadanda ke cikin tashin hankali.