Wayar da kan mutane ta fuskar kiwon lafiya
July 19, 2017Wadannnan cututtuka dai na zama barazana ga jama'a musamman mazauna yankunan karkara wadanda ba sa samun bayanai a kan yadda za su kare kansu daga cututtukan. A yanzu haka dai wannan matashi mai suna Abdurrahim Muhammad Ma'aji na karatun digiri a fannin likitanci a wata jami'a da ke kasar Sudan ta kudu. Ya shaida wa DW cewar irin yadda ya ga matasa a kasar Sudan ta Kudu na taimakawa al'ummarsu shi ne ya ba shi sha'awar shi ma ya dawo gida ya ba da ta shi gudunmawar.
Mutane da dama da suka amfana da wannan talalfi dai sun ce kungiya da wannan matashi ya kafa na da amfani kuma ta na taimakawa mutane kwarai da gaske kan fadakarwar da suke. Binciken da DW ta yi ya nuna cewa irin wannan gudunmawa da Abdurrahim da tawagarsa ke badawa a jihar ta Katsina samun jinjina tare da fatan samun yabo daga lunguna da sakuna na Najeriya.