Wata 'Yar scotland ta kamu da cutar Ebola
December 30, 2014Wata ma'aikaciyar lafiya na yankin Scotland ta harbu da kwayar cutar Ebola dake saurin kisa. Tuni ma dai aka kebeta a wannan Talatar bayan da bincike ya tabbatar da ita a matsayin mutum na farko da ya kamu da wannan cuta a Birtaniya.
Ita dai wannan nas ta na yi wa kungiyar agaji ta Save The children aiki ne a kasar Saliyo, inda ake jin cewa ta harbu da kwayar cutar. Za a yi wa daukacin mutane 71 da suka yi mu'amala da ita gwaji don ganin cewa ko sun kamu da cutar ko a'a. Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun yaduwar Ebola a wurare uku a Saliyo..
Alkaluman da Hukumar Lafiya ta duniya ta fitar sun nunar da cewa kusan mutane dubu takwas cutar Ebola ta yi ajalisun a duniya cikin watanni 12 na baya-bayannan, yayin da mutane dubu 20 suka harbu da kwayar cutar ta Ebola.