Wata Kotu a Indiya ta hukunta masu laifin aikata fyaɗe
August 31, 2013Shi dai wannan matashin ya na ɗaya daga cikin gungun mutane da suka sace matar a cikin motar safa a birnin Delhi tare da yi mata fyaɗen da ya yi sanadin sheƙawarta lahira.
Ana ci gaba da gudanar da shari'ar sauran waɗanda ake zargin da su da laifin waɗanda suka mallaki hankalin kansu. Bisa ga dokokin ƙasar ta Indiya dai, za a iya yanke ma waɗannan mutane huɗu hukucin kisa idan aka same su da laifi. Tuni ma dai ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da laifin fyaɗen ya rigaya ya rataye kansa a gidan yari. Wannan fyaɗen dai ya janyo tofin Allah tsine daga sassa daban-daban na Indiya, inda waɗanda suka gudanar da zanga-zanga game da wannan batu suka yi kira da a rataye waɗanda suka aikata fyaɗen.
Mawallafi : Mouhamadou Awal Balarabe
Edita : Abdourahamane Hassane