Wasu 'yan Nijar sun yi na'am da juyin mulki
August 3, 2023Kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce daruruwan masu zanga-zanga sun amsa kiran gamayyar kungiyoyin farar hula ta M62, wajen mutunta ranar bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga kasar Faransa, wacce ta girke sojoji kusan 1,500 a kasar.Masu zanga-zangar sun ta rera kalaman batanci ga Faransa duk da taimakawa da ta yi wajen yakar kungiyoyin masu ikirarin jihadi, yayin da a daya hannun kuma suka yi ta daga tutotcin Rasha don neman ta shigo Nijar. Wannan kasa da ke da arzikin man fetur da Uranium tana fuskantar katsewar taimako da hulda daga kasashen ECOWAS ko CEDEAO da cibiyoyin kasa da kasa da suka saba taimaka mata tun bayan juyin mulki.
Shi kuwa shugaban kasar Amirka Joe Biden ya yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da iyalansa, wanda ake tsare da su tun lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a kasar. A cikin wata sanarwa da ya fitar yayin bikin cikar Nijar shekaru 63 da samun 'yancin kai daga Faransa, Biden ya nemi da a kiyaye tsarin dimokuradiyya da aka gaggwarmaya wajen tabbatar da shi a Nijar. Sannan shugaban na Amirka ya jaddada muhimmancin hulda tsakanin kasarsa da Nijar, inda ko a waran Maris sai da sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya gana da hambarrarren Shugaba Bazoum.
Ita kuwa Faransa ta sanar da kammala aikin kwashe Faransawa da 'yan kasashen Turai daga Jamhuriyar Nijar, duk da cewa ba a sanar da ainihin adadin wadanda aka kwashe ba. Amma sakon da aka wallafa ta shafin X (Twitter) na cewa Faransawa da 'yan kasashen waje 1,079 da suka hada da Turawa na cikin kykkyawan yanayi na tsaro .