Himalaya: Masu hawa tsauni sun mutu
June 3, 2019Talla
Tun bayan da aka daina jin duriyar mutanen aka bazama gudanar da aikin ceto, sai dai ruwan sama hade da iska mai karfi ya janyo tsaiko wajen gudanar da aikin ceton. Bayan gano gawarwakin mutanen biyar, yanzu ana fatan a koma laluben sauran. A daya bangaren kuma, gwamnatin kasar ta sanar da batan wani jirgin soja da ke dauke da mutane 13. Rahotanni sun nunar da cewa karfe daya da rabi na agogon kasar ya kamata a ce jirgin ya sauka, amma kawo yanzu babu labarinsa. Akwai ma'aikatan jirgi takwas da kuma wasu fasinjoji da ba a kai ga bayyana sunayensu ba ya zuwa wannan lokacin cikin jirgin.