Sanatoci 15 sun fice daga APC
July 24, 2018Talla
A Najeriya 'yan majalisar dattijai fiye da 15 na Jam'iyyar APC mai mulki sun fice daga Jam'iyyar sun koma babbar jam'iyyar adawa PDP a wani mataki da ake gani na kalubalantar takarar shugaban kasar Muhammadu Buhari.
Shugaban Majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ya sanar da hakan ba tare da yin wani karin haske ba.
Daga cikin sanatocin da suka fice daga jam'iyyar dai sun hada da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon gwamnan Jihar Kano.
Matakin na zuwa ne yan makonni bayan da wani tsagi na jam'iyyar ta APC ya sanar a wannan watan cewa ya dawo daga rakiyar gwamnatin.