1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu mutane sun mutu a Tekun Libya

November 23, 2019

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya, ta ce an tsinci gawarwaki shida na wasu masu kokarin shiga kasashen Turai ta tekun Bahar Rum, bayan sun baro Libiya.

https://p.dw.com/p/3Ta7i
Mittelmeer «Open Arms» rettet 73 Migranten
Hoto: Reuters/J. Medina

A wani sakon da ta wallafa a shafinta na twitter, hukumar ta ce an kuma yi nasarar kubutar da wasu bakin hauren su 90 a gabar ruwan Libiyar.

Libiya dai ta zama wata matattarar masu neman shiga Turai daga wasu kasashen Larabawa da kuma Afirka, wadanda ke neman abin da suke kira rayuwa mai inganci.

Galibi dai mutanen na daukar kasada a rubabbun kwale-kwale da a karshe ke fashewa a kan tekun.

Daruruwan mutane ne dai ke rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon wannan bakar hijira da suke yi ta neman shiga kasashen Turai.