1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wassani: Bayer Leverkusen na dab da lashe gasar Bundesliga

Suleiman Babayo
April 9, 2024

Kungiyar kwallon kafa ta Bayer Leverkusen ta tasamma lashe gasar Bundesligar kasar Jamus a karon farko a tarihinta, bayan tazarar maki 16 da ta bai wa mai rike da kambu Bayern Munich.

https://p.dw.com/p/4eZCJ
Fußball Bundesliga | Bayer Leverkusen vs Bayern München
Hoto: Martin Meissner/AP Photo/üicture alliance

Bari mu yaye labulen shirin da yadda Bayer Leverkusen ta yi Bayern Munich fintinkau da tazarar maki 16 a gasar Bundesliga, har ma ta fara jin kamshin lashe kofin a karon farko cikin tarihinta. Inda a karshen mako ta yi tattaki zuwa Berlin ta doke Union Berlin da ci daya mai ban haushi. Yayin da ita kuma Bayern Munich ta kwashi kashinta a hannun Heidenheim da ci 3-2.

Dortmund-Stuttgart 0-1

Eintracht- Bremen 1-1

Mainz-Darmstadt 4-0

Wolfsburg-Monchengladbach 1-3

Cologne-Bochum 2-1

Freiburg-RB Leipzig 1-4

Hoffenheim-Augsburg 3-1

Kakar wasanni ta Shekarar 200172002 ba ta zo wa Bayer Leverkusen da dadi ba, sakamakon ta leko ta koma har sau 4 da ta gani. Real Madrid ta doke ta a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai wato Champions League. Borussia Dortmund ta sha gabanta da maki taya tak wajen lashe Bundesliga, Schalke kuma ta caskara ta a wasan karshe na cin kofin kalubale na Jamus wato Pokal Cup.

Fußball Premier League Manchester United v FC Liverpool
Gasar Firimiya: Mancester United da FC LiverpoolHoto: Dave Thompson/AP/picture alliance

Yanzu kuma sai Firmiyar kasar Ingila ta mai horas da 'yan wasan Manchester United ke shan caccaka kan salon aikinsa, la'akari da yadda kullum kungiyar ke kora komawa baya. Ko da yake a karshen mako ta yi canjaras da babbar abokiyar hamayyarta Liverpool da ci 2-2, amma dai Erik ten Hag ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa yana nan daram a Old Trafford. Arsenal da Liverpool dai na da maki saba'in da dai-dai a saman teburi, yayin Man City ke take musu baya da maki 70.

A Serie A din Italiya Juventus ta doke Fiorentina 1-0, AC Milan vs Lecce 3-0, Mnza vs Napoli 2-4, Roma-Lazio 1-0.

Masana harkokin wasanni na ci gaba da sukar gwamnatin jihar Kano dangare da tabarbarewar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ke fuskanta makonni dai Pillars na fuskantar koma-baya, inda a baya bayan nan ta sha kashi a hannun abokiyar hamayyarta Enyinma da ci 5-0, lamarin da ya janyo cecekuce a Kano.

Novak Djokovic
Noval DjokavicHoto: Antonio Calanni/AP Photo/picture alliance

Daga fagen kwallon Tenis kuwa lamba daya a duniya Novak Djokovic ya ce babban burinsa yanzu shi ne lashe lambar zinariya a gasar Olympics da za a gudanar a birnin Paris a cikin watan Yuli mai zuwa, kasancewar bai taba yin nasara a wannan gasa ba, in banda lambar tagulla da ya taba samu a Beijin a shekarar 2008.

Bari kuma mu karkare da labarin gwanjon gajeren wandon da fitaccen zakaran damben duniya Muhammad Ali, wanda ya yi amfani da shi a shekarar 1975 lokacin da ya doke Joe Frazier, a fafatawar da aka yi wa take "Thrilla in Manilla", a ranar Alhamis mai zuwa za a fara gwamnjon har zuwa Juma'a, da ake sa ran kudin zai haura Dala miliyan 6 ta Amurka.))

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani