1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bochum ta yi wa Bayern wankin babban bargo

Suleiman Babayo RGB
February 14, 2022

Shirin ya kunshi sakamakon wasannin Bundesliga dana Olympics, da yadda harkokin wasanni ke ci gaba da farfadowa a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya inda zaman lafiya ke karfafa sannu a hankali.

https://p.dw.com/p/470NZ
Fußball Bundesliga | FC Bayern München - VfL Bochum
Bochum ta lallasa Bayern da ci 4-2Hoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

A gasar Bundesliga ta Jamus, inda Union Berlin ta sha kaye a gida a hannun Borussia Dortmund 3 da nema, haka ita ma Wolfsburg ta bi Eintracht Frankfurt ta lallasa ta da ci biyu da nema, kana Borussia Moenchengladbach ta doke Augsburg da ci 3 da 2. Sannan Freiburg ta tashi 1 da 1 da Kungiyar Mainz. Ana ta bangaren kungiyar Bayer Leverkusen ta doke Stuttgart 4 da 2.

Nasarar da ta fi daukar hankali da mamaki, ita ce, yadda Bochum ta lallasa FC Bayern Munich da ci 4 da 2. Yan wasan na Bochum sun taka rawar gani a wasan inda zaratan matasan kungiyar suka shirga kwallaye hudu a ragar Bayern. Inda ba a manta ba, a karawarsu ta karshe kafin na karshen makon, Bayern ta doke Bochum da ke mataki na goma sha daya a teburin Bundesligan da ci bakwai da nema.

UK Fußball Premier League | Ägypter Mohamed Salah Afrikas Fußballer des Jahres
Mo Salah na LiverpoolHoto: picture-alliance/dpa/PA Wire/P. Byrne

A wasannin lig Premier da ake karawa a Ingila, Kungiyar Burnley ta tashi 1 da 1 da Kungiyar Manchester United, haka Norwich ta tashi 1 da 1 da Kungiyar Crystal Palace, kana Manchester City da doke Brentford 2 da nema, yayin da Liverpool ita ma ta doke Leicester 2 da nema, sannan Aston Villa da Kungiyar Leeds sun tashi 3 da 3.

Africa Cup of Nations | Burkina Faso v Tunisien
Magoya bayan Burkina Faso a yayin gasar cin kofin AfirkaHoto: DANIEL BELOUMOU OLOMO/AFP

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Burkina Faso ta bayyana cewa, ba za ta kara wa'adin mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Kamou Malo da kwantiraginsa zai kare cikin wannan wata na Febrairu ba. Wannan mataki na zuwa duk da kwazon da 'yan wasan kwallon kafa na kasar suka nuna, a gasar neman cin kofin kwallon kafar nahiyar da aka kammala a kasar Kamaru, inda kasar ta Burkina Faso ta kai wasan kusa da na karshe.

Kasar Beljiyam har yanzu tana mataki na daya a jerin gwanaye kasashe kan kwallon kafa da hukumar kula da wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar, a matsayi na biyu akwai kasar Brazil sannan Faransa tana ta uku, Ajentina ta hudu, Ingila ta biyar, kana Senegal wadda ta lashe gasar cin kofin kasashen Afirka tana matsayi na 18 kuma ta farko a Afirka mataki mafi kololuwa da kasar ta taba samu.

China | Olympische Spiele 2022 | Skispringen Team | Österreich
Gasar Olympics ta 2022Hoto: Hannah Mckay/REUTERS

A wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic na lokacin hunturu da ke wakana a birnin Beijing na Chaina, teburin ya nuna kasar Norway ke kan gaba da zinare 9, yayin da Jamus take matsayi na biyu da zinare 8, a matsayi na uku akwai Amirka mai zinare 7, yayin da Chaina mai masaukin baki ke da zinare 4 a mataki na takwas, sannan Faransa tana matsayi na tara da zinare 3.

A Najeriya, bayan kwashe shekaru cikin matsalolin tsaro da ake alakantawa da Boko Haram wanda ya gurgunta kusan dukkanin harkoki na rayuwa, harkokin wasanni sun farfado kuma su na bunkasa inda ake gudanar da gasa dabam-dabam da ke samun halartar baki daga wajen jihar, kamar yadda za a ji a cikin rahoton da Wakilinmu Al-Amin Suleiman Mohammad ya hada mana daga birnin Maiduguri.