Wasanni: Schalke na ci gaba da samun koma baya a Bundesliga
January 4, 2021Kungiyar kwallon kafar Schalke 04 ta sake shan kashi ci 0-3 a hannun Hertha Berlin, lamarin da ke zama jerin wasannin 30 da ta buga ba tare da nasara a gasar Bundesliga ba. Rabon ita Schalke 04 ta samu nasara tun 17 ga watan Janairu 2020, inda ta doke Mönchengladbach da 2-0. A yanzu ma haka Schalke 04 na da maki hudu kacal a wasanni 14 da ta buga a kakar bana. Idan ba ta samu nasara a wasanta na karshen mako mai zuwa ba, za ta kafa tarihi mafi muni na zama kungiyar Bundesliga da ta buga wasanni 31 ba tare da samun nasara ba. Alhali Schalke na daga cikin kungiyoyin da suke fada ana ji a fagen kwallon kafar Jamus, inda ta taba zama zakara sau da dama na Bundesliga. Sannan a shekarun 2000, Schalke 04 ta kasance mataimakiyar zakaran Jamus sau 5, a karo na karshe a 2017-18.
Tuni ma Schalke 04 take fadi tashi don neman wa kanta mafita, lamarin da ke sa ta sauya masu horaswa. A lokacin hutun hunturu ma dai, kungiyar ta sami sabon mai horaswa dan kasar Switzerland, Christian Gross, wanda ke zama kocinta na hudu a shekara guda.
A sauran wasannin mako na mako 14 kuwa a ranar Asabar, Leipzig ta doke VfL Stuttgart da ci 1-0, kwallon da dan wasan Spain Dani Olmo ya ci a minti na 67. A yanzu dai Leipzig ta dawo matsayi na biyu da maki 31 a teburin Bundesliga, yayin da Yaya Babba take ci gaba da jan zarenta a saman teburi da 33 bayan da ta yi kaca-kaca da Mainz 5-2. Yaya karama ma Borussia Dortmund ta farfado inda ta lallasa Wolfsburg da 2-0, lamarin da ya sata dawowa cikin rukunin biyar na farko. Ita kuwa Bielefeld ta sha kashi ci 1-0 a wasan da suka fafata a gidan Borussia Mönchengladbach, yayin da Union Berlin ta doke Werder Bremen 2-0. Ita ma Cologne ta sha kashi da ci 0-1 a hannun Augsburg.
Kungiyar Freiburg ta yi abin ban mamaki inda ta doke Hoffenheim ci 3-1. Sannan kuma Eintracht Frankfurt ta samu nasarar ci 2-1 a kan Bayer Leverkusen, godiya ta tabbata ga dan wasan Leverkusen wanda ya zura kwallo a gidansu.
A kasar Ingila, a daidai lokacin da aka gudanar da mako na 17 na Premier League, damuwa na dada karuwa tsakanin manajojin kulab din kwallon kafar kasar sakamakon yaduwar annobar covid-19. Fiye da mutane 600,000 sun kamu da cutar corona a makon da ya gabata, kuma hukumomin kiwon lafiya na Ingila na kallon wasannin kwallon kafa a matsayin wuraren taron jama'a da ke yada cutar. Manajan Liverpool, Bajamushen nan Jürgen Klopp yake tunani:
"Mun yi iya kokarinmu don ganin cewar gasar ta ci gaba. Ina ganin cewa matakan na aiki yadda ya kamata. Mun sani cewa a lokacin hunturu watakila za a samu karo na biyu na yaduwar kwayar cutar. Don haka ban yi mamakin karuwar kamuwa da ita ba. Ina ganin za mu iya ci gaba a haka, amma ni ba kwararre ba ne, saboda haka ina mutunta duk shawarar da aka yanke da matakan da za a dauka a makonni masu zuwa."
To daga kwallon kafa, sai kuma wani wasa mai matukar muhimmanci a kasar Hausa, wanda ba wani ba ne illa dambe. Kusan dai mako guda maza suka kwashe suna gurzar juna a Katsina a gasar wasan damben gargajiya na wasu jihohin arewacin Najeriya. Ko da shi ke dai 'yan asalin Sokoto da Kebbi suna sahun wadanda suka saba nuna bajinta idan aka daure hannu, amma a wannan karon 'yan damben Nasarawa ne suka zo na daya, yayin da 'yan Katsina masu masaukin baki suka zo a matsayi na biyu, su kuwa 'yan Jigawa suka kafa murhu a matsayi na uku.