1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Shirin gasar cin kofin kwallon kafa

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
October 16, 2023

Najeriya na ci gaba da daura damarar tunkarar gasar AFCON da wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, yayin da kasashen Turai ke kokarin samun tikitin shiga gasar kwallon kafar nahiyar.

https://p.dw.com/p/4XbHO
AFCON | Najeriya
'Yan wasan kwallon kafar Najeriya, sun samu nasarar shiga gasar AFCON a banaHoto: Sports Inc/empics/picture alliance

Wasannin sada zumunta sun fara gudana a Afirka, a daidai lokacin da ya rage watanni uku a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar a kasar Côte d' Ivoire kana wata guda kafin wasannin share fage na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya. Kungiyar Black Stars ta  Ghana ta yi tattakin zuwa Mexico na yankin Latin Amirka, inda ta sha kashi da ci biyu da nema yayin da Côte d' Ivoire ta tashi kunnen doki daya da daya da da Maroko. Burkina Faso da kyaftin dinta Bertrand Traoré bai buga ba saboda da rauni, ta sha wahala a hannun Equatorial Guinea ko da yake an tashi wasan canjaras babu ci. Ita kuwa Super Eagles ta tashi biyu da biyu da Saudiyya a wasan sada zumunta na farko, ko da yake tawagar na neman gwada 'yan wasanta a shirin neman shiga gasar kofin duniya bayan fafatawa da Lesotho da kuma Zimbabwe a watan Nuwambar da ke tafe. Najeriyar dai ta samu ta samu kanta a rukuni daya da mai masaukin baki Côte d' Ivoire a gasar ta AFCON, lamarin da masana harkokin kwallon kafa ke ganin cewar da jan aiki a gabanta a fannin cike gibi a fannoni da dama idan tana son taka rawar gani a watan Janairu mai zuwa a Côte d' Ivoire.

Jamus | Julian Nagelsmann | Nasara | Kwallon Kafa
Sabon mai horas da 'yan wasan kwallon kafar Jamus Julian NagelsmannHoto: Christian Kaspar-Bartke/Getty Images/Getty Images

Ita ma dai Jamus ba a barta a baya ba a wasanni sada zumuntar, inda  za ta kara da Mexico a ranar Talatar da ketafe bayan da ta doke Amurka da ci uku da daya a karon farko karkashin sabon mai horas da 'yan wasant Julian Nagelsmann. Wannan nasarar ta kwantar da hankalin magoya bayan kungiyar ta Mannschaft, watanni takwas gabanin gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai da za a shirya a Jamus a 20224. A ci gaba da tankade da rairaya kuwa Faransa ta samu gurbin shiga gasar kwallon kafa ta kasashen Turan da za ta gudana a Jamus bayan da ta doke kasar Holland da ci biyu da daya, godiya ga tauraron kwallon Faransa Kylian Mbappé da ya zira wadannan kwallaye da suka dadada ran mai horas da 'yan wasan Didier Deschamps. Ita ma Spain da ke rukuni "A" ta cancanci shiga gasar ta Turai bayan da ta mamaye abokiyar hamayyarta Norway da ci daya da nema, lamarin da ya ba ta damar raka Jamus da Scotland. A rukunin D kuwa, Turkiyya ta lallasa Latviya da ci hudu da nema, yayin da ita ma Romaniya ta doke Andorra da ci hudu da nema. A nata bangaren Wales ta ci Croatia da ci biyu da daya, kana an yi ruwan kwallaye a karawar da aka yi tsakanin Switzerland da Belarus da ci uku da uku.

Jamus | Bayern Munich |  Leroy Sane
Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Bayern Munich ta Jamus Leroy SaneHoto: opokupix/IMAGO

A kasuwar musayar 'yan wasan kwallon kafa, har yanzu kungiyar Bayern Munich ba ta jitu da Liverpool kan kudin da za ta sayar da zakukurin dan wasanta Leroy Sane ba, amma dai Bajamushen zai iya zama dan kwallo mafi tsada da Liverpool ke son saye domin maye gurbin Mohamed Salah a nan gaba. Ita kuwa Inter Milan ta Serie A ta ce ba ta rufe wa tsohon mai tsaron ragarta dan asalin Kamaru Andre Onana kofa ba, duk da rashin taka rawar gani da ya yi a Manchester United. A bangarenta Barcelona ta Spain ta nuna kwadayin sayen Jadon Sancho na Manchester United, matukar dai ba a tsawwala farashinsa ba.

Faransa | Kwallon Zari-ruga | Rugby | Afirka ta Kudu | Nasara
'Yan kwallon zari-ruga na Afirka ta Kudu, sun kai wasan kusa da na karshe a FaransaHoto: Simon King/Pro Sports Images/IMAGO

A fagen kwallon zari-ruga, inda Afirka ta Kudu ta hambarar da Faransa da ci 29 da 28 a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin kwallon zari-rugar ta duniya da ya gudana a Stade de France da ke kusa da birnin Paris. Wannan nasarar ta bai wa Springboks da ke rike da kofin duniya damar hayewa wasan kusa da na karshe, inda za ta kara da Ingila a ranar 21 ga wannan wata na Oktoba. Hasali ma dai, Ingila ta sha wahala kafin ta kai ga doke Fiji da 30 da 24. Ita kuwa New Zealand ta yi tsayuwar daka a karawar da ta yi da Ireland kuma ta yi nasara da ci 28 da 24, lamarin da zai bai wa All Blacks damar tinkarar Argentina a wasan kusa da na karshe a ranar 20 ga watan na Oktoba a yunkurinta na neman lashe kofin duniyar na  kwallon zari-rugar a karo na hudu. Da ma Argentina ta bai wa Wales mamaki, inda ta fitar da ita daga gasar da ci 29 da 17.