Jamus ta kai zagaye na gaba a Euro 2024
July 1, 2024An shiga zagaye na biyu na wasannin neman lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Turai Euro 2024 da ke gudana a nan Jamus, inda aka gudanar da wasannin da sakamakonsu ba su zo da mamaki ba. Kamar yadda aka yi hasashe tun da farko, Spaniya ta gasawa sabon shiga Jojiya aya a hannu da ci hudu da daya a birnin Cologne. Abin mamakin ma shi ne yadda Robin Le Normand na Jojiya ya shammaci mai tsaron gidan Spaniya, inda ya zura masa kwallo a mintuna 18 da fara wasa. Sai dai bayan da La Roja ta farfado zakakuran matasan 'yan wasanta masu kwazo wato Nico Williams mai shekaru 21 da Lamine Yamal mai shekaru 16 sun rinka saba kwallo suna juya ta, lamarin da ya bai wa Spaniyan damar mamaye wasan tare da samun rinjayen kwallo. Sai dai duk da wajen road da aka yi da ita, Jojiya ta taka rawar gani a wannan gasa da ke zama karon farko da ta shiga bisa jagorancin tsohon dan wasan Bayern Munich Willy Sagnol musamman ma a karawar da Turkiyya da Portugal. Ko da Georges Mikautadze daya daga cikin wadanda suka ci wa Jojiya kwallo, sai da ya yi alfahari da bajintar da kasarsu ta nuna.
A wasan daf da na kusa da karshe wato quater finals dai, Spaniyan za ta kara ne da Jamus mai masaukin baki wacce ta fuskaci kalubale da yammacin ranar Asabar a Dortmund wajen kawar da kasar Denmark da ci biyu da nema. Babu arkanar da ba a gani a wannan wasa ba, kama daga guguwa da ruwan sama mai karfi da ya tilasta alkalin wasa dakatar da wasan na dan lokaci har zuwa soke kwallon Denmark da amfani da na'urar VAR wajen bai wa Jamus bugun daga kai sai mai tsaron gida. Amma dai a karshe Kai Havertz da Jamal Musiala sun share wa Jamus hawaye ta hanyar zura kwallayen biyu a raga, lamarin da mai horas da Mannaschaft Julian Nagelsmann ya ce abin a yaba ne domin sun kai su mataki na gaba. Babbar kungiyar kwallon kafar Jamus na daga cikin wadanda suke daukar hankali a nahiyar Afirka, kasancewar ta kunshi 'yan wasa da ke da tsatso da Afirka kamar Jonathan Tah ko Leroy Sane. Ko da a Ghana ma, ma'abota kwallon kafa na bibiyar gasar ta Euro 2024 ta Jamus ke shiryawa sau da kafa, saboda Jerome Boateng wanda mahaifinsa dan asalin wannan kasa ne ya taba kare martabar babbar kungiyar kwallon kafar Jamus abin da ya sanya suke fata Jamus ta ci gaba da taka rawar gani.
Ita kuwa Ingila ta fara ganin rashi kafin ta ga samu a wasan da ta yi da Slovakiya, duk da tarin taurari da take da su kamar Jude Bellingham da Harry Kane. Slovakiya ce ta fara cin kwallo ta hannun Ivan Schranz a mintuna na 25 da fara wasan, amma sai har a mintunan karshe bayan karin lokaci ne Jude Bellingham ya rama wa kura aniyarta. Dadin dadawa ma dai, Harry Kane ne ya sanya kwallo a raga da ka, lamarin da ya bai wa Ingila nasara a wasan da ci biyu da daya. Sai dai daya daga cikin 'yan wasanta na baya Ezri Konsa ya yi alkawarin cewa, za su zage damtse a wasansu na gaba. A wasan daf da na kusa da na karshe a Düsseldorf, Ingilan za ta kara ne da Switzerland wacce ta yi rawar gani sosai a yammacin ranar Asabar a Berlin da ci biyu da nema a karawar da ta yi da tawagar Italiya da ta kasa tabbatar da matsayinta na zakaran Turai. A sauran wasanni, Faransa na karawa da makwabciyarta Beljiyam a Düsseldorf da karfe shida na yamma yayin da Portugal da Soleveniya ke kece raini a Frankfurt.
A ci gaba da gudanar da hada-hadar musayar 'yan kwallon kafa na bazara, Paris St-Germain ta kasar Faransa ta lashe takobin sayen dan wasan gefe na Spaniya Lamine Yamal mai shekaru 16 a duniya da ke taka leda a kungiyar Barcelona. PSG ta ce a shirye take ta zarta kudin da ta sayi Kylliam Mbappe da sauran manyan 'yan wasa, wajen sayen Yamal wanda yake wuta a gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Turai duk da cewa ko sakandare bai kammala ba. Ita kuwa Manchester City ta dana tarkonta ne a Jamus, inda take son a cefanar mata da dan wasan tsakiya na Bayern Munich Joshua Kimmich da Dani Olmo na RB Leipzig da ke wasa a gefe. A bangarenta, Juventus ta Italiya ta sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyar da Douglas Luiz daga Aston Villa. Dama dai dan wasan na tare da Brazil, inda ake buga gasar Copa America a kasar Amurka.