1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani hari ya salwantar da mutane a Mali

September 23, 2023

Bayanan da ke fitowa daga birnin Timbuktun arewacin kasar Mali, na tabbatar da salwantar akalla fararen hula biyar a wani hari na baya-bayan nan da aka kai kan al'uma.

https://p.dw.com/p/4Wjnh
Hoto: Getty Images/Stringer

Sabon harin da cikakkun bayanansa ke fitowa a wannan Asabar bayan kai shi a ranar Alhamis, ya zo ne wata guda da rabi bayan kawanyar da mayakan tarzoma suka yi wa Timbuktun.

Tabbacin harin ya fito cikin wata hirar da gwamnan yankin Bakoun Kante ya yi da kafofin watsa labaran cikin kasar, kuma ya ce tuni aka yi jana'izar wadanda suka mutun.

Wasu cibiyoyin lafiya ma dai sun ruwaito cewa akwai sama da mutum 20 da suka jikkata a harin.

Daga cikin wadanda suka salwantan kuma har da wasu kananan yara, kamar yadda shaidu suka tabbatar.