Wani farmaki ta sama da Turkiya ta kai ya halaka Kurdawa 34
October 24, 2007Talla
Dakarun kasar Turkiya sun yi lugudan wuta akan wuraren da ake zargi na kungiyar ´yan tawayen Kurdawa na PKK ne dake kan iyakar da Iraqi inda suka halaka mutane 34. Wata majiyar soji ta fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa a jiya daddare jiragen saman yakin Turkiya sun kutsa cikin wani yankin Iraqi mai tazarar kilomita 20 daga kann iyakar kasashen biyu. A kuma halin da ake ciki sojojin kasa na Turkiya kimanin 300 na kara dannawa zuwa wannan yanki. A jiya talata FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce ba zai jira har abada ba kafin gwamnatin Iraqi ta dauki wani mataki kan ´yan tawayen wadanda suka halaka dakarun Turkiya 12 a ranar lahadi da ta gabata ba. A kuma halin da ake ciki an ba da umarnin rufe dukkan ofisoshin jam´iyar ma´aikatan Kurdawa dake cikin Turkiya baki daya.