1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilan SPD sun goyi bayan gwamnatin haɗin gwiwa da CDU

December 14, 2013

Bayan gudanar da ƙui'ar jin ra'ayin yan jam'iyyar Social Democrats, wato SPD a nan Jamus, fiye da kashi biyu cikin kashi uku na wakilan sun amince da gwamnatin ta haɗin gwiwa

https://p.dw.com/p/1AZp2
Hoto: John MacDougall/AFP/Getty Images

Yanzu dai babu sauran abin da ya rage da zai hana rua gudu a shirin kafa gwamnatin hadin gwiwa ta manyan jam'iyyu a nan Jamus.

SPD ta sanar da ƙuri'ar ra'ayin jama'ar da ta yi kan kafa gwamnatinhaɗaka

Ranar Asabar jam'iyyar Social Democrats,wato SPD ta sanar da sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayi da ta gudanar tsakanin wakilanta, game da kafa gwamnatin ta haɗin gwiwa tsakaninta da jam'iyyun CDU da CSU da za ta yi mulkin tsawon shekaru huɗu masu zuwa. Barbara Hendrichs ke nan, wadda aka ɗanka mata alhakin kula da ƙidaya ƙuri'un wakilan na jam'iyyar SPD take gabatar da sakamakon da ƙuri'un na jin ra'ayi ya haifar, inda tace kashi 75 da ɗigo 96 ne na wakilan suka amince da kafa gwamnatin ta haɗin gwiwa tsakanin SPD da CDU da CSU, yayin da kashi 23 da digo 95 suka yi adawa da haka.

Nan gaba kaɗan za a kafa gwamnatin ƙawance

Jim kaɗan bayan da Heindrichs ta sanar da sakamakon ƙuri'ar, gaban manyan shugabannin jam'iar ta SPD, ciki har da janar sakatar, Andrea Nahles da shugaban wakilan SPD a majalisar taraiya ta Bundestag, Frank-Walter Stinmeier, shi kansa shugaban jam'iyyar, Sigmar Gabriel, cike da farin ciki ya baiyana godiya ga dukkanin wakilan jam'iyarsa, musamman kuma waɗanda suka taimaka ƙui'ar ta jin ra'ayin ta gudana. A game da sakamakon da aka samu Gabriel ya nuna cewa:

Ya ce ''Wannan dai babban biki ne da ya nuna yadda demokraɗiyya ta ke aiki a cikin jam'iyyarmu, kuma babban biki ne da ke nunar da yadda demokraɗiyya ma gaba ɗaya take aiki. Ina kuma da ra'ayin cewar wannan rana ba ma a tarihin tsarin Social Democrats na Jamus ne ka ɗai za ta ɗauki hankali ba, amma ina ganin har ma ranar za ta zama ta tarihi a tafarkin demokraɗiyyaa Jamus baki ɗaya.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita Abrourahmane Hassane