Waiwayen shekara ta: 2023 cikin hotuna
Yake-yake, da rikice-rikice gami da bala'oi suna cikin abubuwan da aka fuskanta a shekara ta 2023. Tashar DW ta duba lamarin cikin hotuna.
Kwanciyar kabari
Jami'an kocin Vatikan biyu suke shirya makarar Maraigayi tsohon Fafaroma Benedikt XVI ranar biyar ga watan Janairu. Daga bisani dubban mutane masu zaman makoki suka kalli wucewa da gawar a dandanlin St. Peter domin ban-kwana. A shekara ta 2013 Marigayi Benedikt XVI ya zama Fafa-Roma na farko cikin karni shida da ya yi murabus daga ofis bisa dalilan rashin lafiya - galibi fafaroma kan mutu a ofis.
Mamaye majalisar dokoki
Daruruwan magoya bayan Jair Bolsonaro tsohon shugaban kasra Brazil sun mamaye majalisar dokokin da ke birnin Brasilia ranar takwas ga watan Janairu tare da haddasa barna. Kwanaki gabanin haka magajin Bolsonaro wato Lula da Silva ya dauki madafun iko. Shi dai Bolsonaro bai fito fili ya amince da sakamakon zaben ba, wanda Kuka ya lashe. An zargin tsohon shugaban da haddasa rudanin.
Hange daga sama
Ranar 11 ga watan Janairu 'yan sanda sun kwashe mutane a garin Lützerath da ke Jamus game da hakar ma'adanai. Za a rusa kauyen domin tonon makamashin kwal. 'Yan gwagwarmyan kare muhalli sun mamaye gidajen da bishiyoyi bisa zanga-zangar adawa da matakin. Amma babu sakamakon da haka ya haifar domin an rushe gidajen na Lützerath bayan kwana biyar.
Ya ki mika wuya
Mesut Hançer yana rike da hannun 'yarsa mai shekaru 15 da haihuwa Irmak, wadda ta rasu sakamakon girgizar kasa a garin Kahramanmaras na kasar Turkiyya. An samu girgizar kasar mai karfi maki 7.8 ranar shida ga watan Febrairu a wasu bangarori na kasashen Turkiyya da Siriya; Fiye da mutane dubu-59 suka halaka kana wasu kimanin dubu-125 suka jikata.
Sarki a shekaru 73
Ya dade yana jira game da lokaci mai girma, na gadon sarautar Birtaniya, kuma a watan an yi bikin sarautar Sarki Charles wanda ya gaji mahaifiyarsa Elizabeth wadda ta rasu a shekarar bara bayan mulkin tsaron shekaru 70. Charles yanzu yana mukkin Birtaniya game da kasashe 14 rainon Birtaniya da suka hada da Australiya, New Zealand da Kanada.
Karkashin kasa
Kasar Ukraine ba yaki daga Rasha kadai take fuskanta ba, amma har da bala'in ambaliyar ruwa. Ranar shida ga watan Yuni an samu fashewa a madatsar ruwan Kakhovka inda ya nutsar da garuruwan da suke da nisan murabba'in kilo-mita 900. Kasashen Rasha da Ukraine sun zargi juna game da abin da ya faru, masu bincike na kasashen duniya sun yi imanin Rasha take da alhakin fashwar da aka samu.
Iftila'i a karkashin teku
Duniya ta kwashe kwana hudu tana jira cikin tsammani: Mutane biyar da ke son ganin tarkacen katafaren jirgin ruwan "Titanic" suna cikin wani karamin jirgin ruwa ranar 18 ga watan Yuni. Amma bayan sa'oi biyu da nutsewa an samu katsewar sadarwa, inda aka fara aikin agajin ceto mai girma. A karshe an gano karamin jirgin ya tarwatse inda mutanen suka mutu.
Yunkuri mai hadari
Galibin mutanen 700 da ke cikin jirgin ruwan sun halaka. Jim kadan bayan jirgin ruwan ya bace, wanda yake shake da bakin haure daga bisani ya kife a gabar tekun Girka. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta yi sukar yadda aka nuna rashin damuwa da kai musu dauki, kamar na karamin jirgin ruwan. Kimanin bakin haure dubu-biyu da dari-500 suka nutse cikin tekun a shekara ta 2023.
Maci a birnin Mascow
A karshen watan Yuni sojojin haya na kamfanin Wagner na Rasha sun fito daga kasra Ukraine inda suke yaki, inda suka nufi birnin Moscow tare da mamaye Rostov-on-Don ba tare da fuskantar tirjiya ba. Kwana daya bayan haka shugaban kamfanin Yevgeny Prigozhin ya bayyana kawo karshen macin zuwa Moscow; Wata biyu daga bisani ya mutu sakamakon hadarin jirgin sama cikin wani yanayin rudani.
Tsira daga wuta
A watan Yuli an kwashe masu yawon shakawa a Rhodes saboda gobarar dajin da aka samu a garuruwan da suke kusa. Kimanin kashi 10 cikin 100 na wuraren yawon shakatawa aka samu gobarar. Wannan gobara ta rasta yankunan Girka kuma ta kasance mafi girma a tarihin kasashen tarayyar Turai. Haka kuma an samu fari gami da matsanancin zafi a galibin kasashen duniya lokacin bazara a shekara ta 2023.
Rusawa
Ranar 10 ga watan Satumba an samu wata mahaukaciyar guguwa mai suna "Daniel" da ta haifar da ambaliyar ruwa a gabar ruwan Girka da Libiya. Haka ya janyo fashewar madatsan ruwa guda biyu kusa da garin Derna na Libiya mai tashar jiragen ruwa inda ruwa ya shafe daukacin wasu sassan garin. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta kimanin mutane dubu-11 suka mutu kana wasu kmanin dubu-35 suka rasa gidajensu.
Gagarumar matsalar gudun hijira
A karshen watan Satumba, kasra Azerbaijan ta kwace iko da yankin Nagorno-Karabakh wanda kasashen duniya ba su dauka a matsayin kasa ba, bayan yakin kwana daya. A karkashin dokokin kasashen dunyia yankin da galibi 'yan kabilan Armeniya suke rayuwa yana bangaren kasar Azerbaijan. Fiye da mutane dubu-100 suka tsere daga yankin inda suka mamaye iyaka da Armeniya.
Ta'addancin zubar da jini
Yahudawa sun fuskanci kisan gilla mafi girma tun bayan Yakin Duniya na Biyu: Ranar bakwai ga watan Oktoba 'yan ta'adda na kungiyar Hamas sun kaddamar da hari kan Isra'ila. Sun harba rokoki daga Zirin Gaza, sannan 'yan ta'adda sun shiga kasar inda suka kashe mutane, da gana azaba da yi wa mata fyade. Sun kashe kimanin mutane dubu da dari 200. Sun yi garkuwa da wasu kimanin 240 zuwa Zirin Gaza.
Azaba a kowane bangare
Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan Zirin Gaza bisa martanin wannan hare-hare na 'yan ta'adda. Fararen huia sun galabaita, inda Hamas ta ce fiye da mutane dubu-10 suka halaka, tana ci gaba da cilla rokoki zuwa Isra'ila. Ana zanga-zanga a kasashe da dama domin neman Isra'ila da tsagaita hare-haren. Ana samun kalaman kiyayya da hare-hare kan Yahudawa - amma har da nuna kin jinin Musulmai.
Gadaje babu kowa alamun mutanen da aka yi garkuwa da su
A birnin Tel Aviv ana tunawa da wadanda Hamas ta yi garkuwa da su. A watan Nowamba, Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta tare da musanyen wadanda aka yi garkuwa da su da kuma Falasdinawa fursunonin da suke Isra'ila. A gaba daya an saki mutane 105 da aka yi garkuwa da su gami da fursunonin 240. Bayan mako guda na tsagaita wuta an koma fada. Akwai kimanin mutane 140 da ake garkuwa da su.
Haduwa a karshe
An kwashe kwanaki 51 Aviv Asher na tunanin iyalansa da Hamas ta yi garkuwa da su. A karshen watan Nowamba, Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta da musanyen wadanda aak yi garkuwa da su da kuma fursunoni Falasdinawa. A gaba daya an saki wadanda aka yi garkuwa da su 105 ciki har da Doron Asher da 'ya'yanta. Mako gudan aka yi na tsagaita wuta, akwai sauran mutane 140 a hannun Hamas..