Bala'iSpaniya
Wadanda suka rasu a ambaliyar Spain sun zarta 200
November 1, 2024Talla
A yankin valencia inda ambaliyar ta fi yin ta'adi mutane akalla 202 suka rasu a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta yankin.
Wasu karin mutane biyu sun rasu a yankin Castilla La Mancha da Andalusia.
Akwai kuma mutane da dama wadanda suka bace har yanzu ba a gano su ba yayin da ake hasashen samun karin ruwa sama mai yawa a 'yan kwanaki masu zuwa.