An yi bankwanan karshe da Paparoma
January 5, 2023Bikin jana'izar ya samu halartar shugabanni addini mabiya darikar Katolika da shugabannin gwamnatoci da kasashe da kuma dumbin mabiya daga sassa daban daban na duniya, ciki har da shugaban gwanantin Jamus Olaf Scholz.
Shagulgulan jana'izar ya gudana ne a karkashin Paparoma Francis wanda ya karbi jagorancin fadar Vatikan daga hannun marigayi Benedikt na 16, bayan ya kafa tarihi na zama jagoran darikar katolika na farko da ya yi marabus a shekarar 2013.
Karin bayani: Mutuwar Benedict na 16 ta girgiza shugabannin duniya
Bayan isowarsa gurin a kekan guragu yana kewaye da kadinal 5, Paparoma Francois ya yi mubaya'a wa gawar wacce ke cikin bakin akwati mai dauke da sunan marigayin na asali da kuma Bible.
"Mun zo a nan da turare mai tsarki don nuna wa marigayin soyayyarmu a gare shi wacce ba za ta taba fita ba daga zukatanmu. Za mu numa masa kauna marar misali cikin girmamawa kamar yadda ya share shekaru masu yawa yana nuna irinta tare da hidimtawa wannan addini. Sai mu ce ya Allah mun mi ka ruhin sa a gareka".
An kwashe sama da awa daya ana addu'a wa gawar wacce sama da limaman cocin 4,000 suka jagoranta, kuma shi ne karon farko a tarihin da wani fafaroma ya halarci jana'izar wani fafaroma. Ga mabiya addinin Krista wadanda suka samu halarta jana'izar bajamushen Fafaroman.