Uwargidan shugaban Nijeriya Stella Obasanjo ta rasu
October 23, 2005Allah yayiwa uwargidan shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo wato Stella Obasanjo rasuwa a yau lahadi bayan an yi mata tiyata a wani asibiti dake kasar Spain. Da a cikin watan gobe Stella Obasanjo zata cika shekaru 60 a duniya. Ba´a ba da karin bayani game da abin da yayi sanadiyar mutuwarta, inji wata sanarwa da fadar shugaban Nijeriya ta bayar. Ita ma ma´aikatar harkokin wajen Spain ta ce uwargidan Obasanjo ta mutu da sanyin safiyar yau lahadi a wani asibiti dake birnin Marbella na kudancin Spain, to sai dai ma´aikatar ta ce ba ta sani ba ko an yi wa Stella din tiyata a asibitin kamar yadda jami´an Nijeriya suka nunar. Ma´aikatar ta ce yanzu haka an aike da gawar zuwa wani ofishin kula da mutuwar ba zato ba tsammani dake Malaga don gudanar da bincike.