1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine ta yi shelar dakile harin jiragen Rasha

April 16, 2024

Rasha ta harba jirage marasa matuka a ci gaba da kai farmaki ba kakkautawa kan Ukraine, duk da cewa ma'aikatar tsaron kasar ta Ukraine ta ce sun yi nasarar kakkabo dukkan jiragen da Rasha ta harba kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4epTJ
Sojojin Ukraine a yayin da suke kakkabo makaman Rasha a Bakhmut
Sojojin Ukraine a yayin da suke kakkabo makaman Rasha a BakhmutHoto: Oleksandr Ratushniak/REUTERS

Kasar Ukraine ta yi nasarar kakkabo dukkan jirage marasa matuka tara da Rasha ta harba kasar a wannan talatar, a cewar ma'aikatar tsaron Ukraine.

Karin bayani: Rasha ta sake kai hari kan tashoshin makashi a Ukraine 

Rasha ta harba galibin makaman ne a yankunan gabashi da kuma kudancin kasar ta Ukraine.

Karin bayani: Kyiv za ta tsaurara tsaro saboda barazanar Rasha 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai tattauna da shugaban kasar Chaina Xi Jinping a birnin Beijing, kan yadda shugabannin kasashen biyu za su hada karfi-da-karfe wajen tabbatar da zaman lafiya a Ukraine.